
Gwamnonin jam’iyyar APC, sun ki amincewa da zaɓar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar na shugabancin ƙasa a zaben 2023.
Da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, jim kadan bayan ganawa da shugaban a Villa, shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, ya ce sun dauki matakin ne na marawa dan takarar Kudu baya domin a samu adalci da zaman lafiya a kasa baki ɗaya.
A cewarsa, mutane 13 daga cikinsu sun nemi afuwar shugaban kasar kan samun bayanin matsayinsu bayan da aka fallasa bayanan.
Lalong ya ƙara da cewa gwamnonin sun dauki matakin goyon bayan sauyin mulki, ko da yake sun sanar da shi cewa dole ne dan takarar shugaban kasa ya fito ta hanyar adalci.
Ya ƙara da cewa shugaba Buhari ya umurce su da su gana da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa, NWC, domin cimma matsaya kan shirin maye gurbin.
Dangane da rashin halartar gwamnan jihar Kogi, ya ce abokin aikin sa ba ya cikin yarjejeniyar domin babu sa hannun sa a cikin sanarwar.
A nasa gudunmuwar gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce hakkin dimokaradiyya ne na gwamnan Kogi ya ba kan sa.