
An sayar da wani littafi da aka yi imanin shi ne na farko kuma mafi cika na baibul na yaren Hebrew akan dala miliyan 38.1 ranar Laraba a birnin New York, in ji gidan gwanjon kaya na Sotheby’s.
Wajen gwanjon na da dukka kwafi 24 na Littafi Mai Tsarki na yaren Hebrew, inda fallen 12 ne kawai su kancire a jikin littatafan kuma sun riga zuwa kafin Littafin baibul na Leningrad Codex, da kusan shekaru ɗari ” in ji gidan gwanjon.
Littafin baibul din, wanda ya kasance a ƙarshen karni na tara ko farkon karni na 10, ya zama rubutun da aka yi gwanjo mafi tsada da kuma kayan tarihi na addinin Yahudawa mafi tsada da aka yi gwanjo a tarihi, in ji Sotheby.
Bayan an gabza a ciniki na mintuna hudu kacal, wata kungiya mai zaman kanta ta Amurka ce ta lashe wannan gwanjon, wadda ta yi niyyar ba da kyautar sa ga gidan tarihin Yahudawa na ANU da ke Tel Aviv.
(dpa/NAN)