Home Kanun Labarai Hadarin jirgin ruwa yayi sanadiyar rasuwar mutum bakwai ‘yan gida daya

Hadarin jirgin ruwa yayi sanadiyar rasuwar mutum bakwai ‘yan gida daya

0
Hadarin jirgin ruwa yayi sanadiyar rasuwar mutum bakwai ‘yan gida daya
Wasu daga cikin gawarwakin da aka ciro a ruwa

Wani mummunan hadarin jirgin ruwa a karamar hukar Yawuri dake jihar kebbi yayi sanadiyar rasuwar mutum tara iyalan mutum guda. Hadarin wanda ya faru a yammacin ranar Litinin da misalign karfe 6 na yamma.

Su dai mutanan sun hau kwale kwale ne domin zuwa kauyen Rukubalo dake yankin karamar hukumar mulki ta Yauwuri a jihar Kebbi, inda daga bisani suna tafiya jirgin ya kife dasu, binciken DAILY NIGERIAN HAUSA ya tabbatar da cewar mutum tara ne iyalan mutum guda suke cikin wannan jirgi.

Bayan da jirgin ya kife da su, anci nasarar tsamo mutum biyu da ransu, yayin da mutum biyar aka dauko gawarwakinsu, inda har ya zuwa yanzu ba’a ga sauran gawarwakin mutum biyu ba.

Malam Abdullahi Rukubalo, shi ne mutumin da iayalnsa gaba daya suka hau wannan kwale kwale day a kife da su. Yana cikin dimuwa sosai a lokacin da aka nemi yin Magana da shi.

An bayyana sunayen wadan da suka rasu kamar haka, Rayyanu Abdullahi da Saadu Abdullahi da Tukur Abdullahi da Sani Abdullahi da Zakiru Abdullahi da Maryam Abdullahi da Madina Abdullahi wadannan sune wadan da aka bayyana cewar sun rasu kuma an samu gawarwakinsu, sauran wadan da suka samu tsira a hadarin sune Yahuza Abdullahi da Babangida Abdullahi.

Wannan dais hi ne karo na uku da aka samu irin wannan hadari wanda yazo da asarar rayuka a yankin karamar hukumar mulkin Yawuri a jihar ta Kebbi.