
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta tarbi maniyyata 955 daga kasashen Indonesia da Bangladesh, wadanda suka wakilci alhazan da suka zo da ga wajen kasar ta filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da na Yarima Mohammed Bin Abdulaziz da ke Madina, a cikin shirye-shiryen da a ka ƙaddamar daga dukkan cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu don yiwa alhazai hidima.
Mataimakin Ministan Hajji da Umrah Dr. Abdelfattah Bin Suleiman ya bayyana cewa, gwamnatin Sarki Salman, Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu masu alfarma, ta yi aiki na tsawon watanni don samar da hidima ingantacciya ga baƙin Allah a yayin aikin Hajjin bana.
Ya kuma jaddada shirye-shiryen ma’aikatar tare da hadin gwiwar dukkanin hukumomin gwamnati wajen kammala dukkan ayyukan mahajjata cikin sauki, tun daga ba da biza, da tabbatar da yanayin kiwon lafiya, da tsara ayyukan canjin masaukai da samar da su tare da hadin gwiwar dukkanin cibiyoyin da ke hidima a aikin Hajji har zuwa lokacin da alhazzai za su koma kasashensu daga kasar Saudiyya bayan kammala ibadarsu.
Ya kuma yi maraba da wakilan mahajjata 405 daga Bangladesh bayan tsaikon da aka yi na tsawon shekaru biyu saboda yanayin annobar korona.
Ya kuma jaddada himmar ma’aikatar don biyan bukatun mahajjata da buri da kuma sauƙaƙe hanyoyin gudanar da ayyukansu. .