Home Labarai Hajjin bana: Gwamnatin Legas za ta mayar wa maniyyatan da basu samu kujera ba kuɗaɗensu

Hajjin bana: Gwamnatin Legas za ta mayar wa maniyyatan da basu samu kujera ba kuɗaɗensu

0
Hajjin bana: Gwamnatin Legas za ta mayar wa maniyyatan da basu samu kujera ba kuɗaɗensu

 

 

 

Gwamnatin jihar Legas ta ce za ta mayar wa da maniyyata aikin Hajji kuɗaɗen su da suka biya amma basu samu kujera ba a Hajjin bana.

Kwamishinan harkokin cikin gida, Prince Anofiu Elegushi, ne ya bayyana hakan a jiya Talata yayin wani taron manema labarai a cibiyar ‘yan jarida ta Bagauda Kaltho da ke Alausa, Ikeja.

Elegushi ya ce za a mayar wa da waɗanda abin ya shafa kuɗaɗen su cikakku, inda ya ƙara da cewa za a yi biyan cikin tsari da kuma gaggawa.

Ya ce gwamnatin jihar Legas za ta buga sunayen maniyyatan da abin ya shafa a a jaridun ƙasa a matsayin rukunin farko na aikin Hajjin 2023.

A cewarsa, gwamnati za ta kuma dakatar da sayar da fom na aikin Hajjin 2023, har zuwa lokacin da za a tabbatar da ainihin adadin kujerun da za a bayar.

Kwamishinan ya tabbatar wa dukkan maniyyatan jihar goyon bayan gwamnatin jihar a kowane lokaci tare da addu’ar Allah ya dawo da alhazan da aka riga aka yi jigilarsu gida lafiya.