
Ƙasar Saudi Arebiya ta sanar da saukar jirgin ruwa ɗauke da raguna 50,000 daga nahiyar Afirka.
Shirin ‘Kingdom of Saudi Arabia Project for Utilization of Hady & Adahi’ ne ya sanar da isowar ragunan zuwa gaɓar ‘Islamic Port’ a birnin Jeddah.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da ragunan ne domin yin hadaya, wacce rukuni ce a cikin rukunnan aikin Hajji.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a watan da ya gabata ne wani jirgin ruwa, ɗauke da dubban raguna, ya nitse a teku a yankin Sudan.