
Tawagar farko ta alhazan Nijeriya ta tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Tawogar ta tashi ne daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke birnin Kebbi na jihar Kebbi.
Gabanin fara jigilar maniyyatan sai da hukumar ta gudanar da wani ƙwarya-ƙwaryar biki ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da kuma Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima.
BBC Hausa