
Wani ɗan Sarki a masarautar Zazzau, Munir Ja’afaru, ya yi murabus daga mukaminsa na hakimin Basawa.
Ja’afaru, wanda kuma ke rike da sarautar Madakin Zazzau, ya yi murabus ne bisa zargin an danne ikon sa a kan naɗin wani Mai unguwa.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Ja’afaru, wanda mahaifinsa, Sarki Jaafaru dan Isyaku shi ma ya yi murabus a matsayin Sarkin Zazzau tsakanin 1937 zuwa 1959, ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu takarar karagar sarautar bayan rasuwar Sarki Shehu Idris a watan Satumban 2020.
Wata majiya mai tushe a masarautar ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa hakimin ya yi murabus ne bayan Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya ki amincewa da nadin Mai Unguwar Gwaba.
“A bisa al’ada, shi Hakimi shi ke zaɓar wanda za a naɗa a matsayin Mai Unguwa, sannan sai a yi bikin naɗin a Zauren Sarki na fadar sarki, daga nan kuma sai a gabatar da shi ga Sarki domin amincewa daga Magatakardan Hakimi.
“Amma a lokacin da aka gabatar wa da Sarki sabon Mai Unguwar Gwaba da aka naɗa don amincewa, sai sarkin ya tambayi dalilin da ya sa Hakimi bai zo wajen ba inda kuma nan take ya ba da umarnin a tube rawanin sabon Mai Unguwar,” inji majiyar.
Kakakin Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu ya tabbatar da murabus din a wata sanarwa da ya fitar, inda kuma bai bayyana dalilan yin murabus din ba.
Ya ce tuni Sarkin ya amince da murabus din sannan ya nada wanda zai maye gurbinsa.