Home Labarai Hakimin Bunkure ya naɗa Adamu Mato a matsayin Turakin Bunkure

Hakimin Bunkure ya naɗa Adamu Mato a matsayin Turakin Bunkure

0
Hakimin Bunkure ya naɗa Adamu Mato a matsayin Turakin Bunkure

 

Galadiman Rano, Hakimin Bunkure, Alhaji Muhammad Isah Umar, ya naɗa Alhaji Adamu A. Mato a matsayin Turakin Bunkure.

A takardar shaidar tabbatar da haɗin sarautar, wacce Hakimin ya sanya wa hannu da kansa a ranar 28 ga watan Febrairu, ya ce an naɗa Mato a matsayin Turakin Bunkure ne a bisa amincewar Mai Martaba Sarkin Rano.

Ya ƙara da cewa a takardar da Sarkin Rano ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Fabrairu, mai lamba REC/BNK/DIST/2/V.l/126, an naɗa Mato Turakin Bunkure ne bisa cancantarsa da kuma biyayya ga masarautar.

Takardar ta kuma taya Mato murna da addu’ar Allah Ya taya shi riƙo.