
Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a jihohi 36 na tarayya da kuma Abuja sun yanke shawarar ganawa da kwamitin koli na jam’iyyar (NWC) da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da ƙasar nan ta shiga.
Daily Trust ta rawaito cewa sakataren kungiyar shugabannin jam’iyyar APC na jihohi kuma shugaban ta a jihar Cross River, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis bayan taron da su ka yi a Abuja.
Ogar, wanda ke tare da shugaban riko na kungiyar, Honarabul Cornelius Ojelabi, da sauran shugabannin jihohi ya ce taron zai tattauna batutuwa da dama da gwamnatin tarayya ciki har da na kuncin rayuwa a kasar.
Ya ci gaba da cewa, “A jiya ne kungiyar shugabannin jam’iyyar APC ta Jihohi su ka yi taro domin tattauna batutuwan da su ka shafi tsarin dimokuradiyyar jam’iyyar da kuma nasarar gwamnatinmu ta APC a karkashin ingantaccen jagorancin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata. Kashim Shettima GCON
Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai kan wahalhalun da kasar ke ciki a yanzu, Ogar ya ce, “Game da kuncin rayuwa, eh, kowa na da korafi. Mu na sane da hakan kuma shi ne mu ka ce za mu yi ganawar sirri da NWC da gwamnati.
“Don haka gwamnatin da muke nufi ita ce gwamnatin tarayya. Har sai an yi faxa da tsifa naga sakamako, amma yanzu ya yi wuri a yi magana da manema labarai kan wadannan batutuwa.”