Home Labarai An hallaka Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari, ƴan ta’addan da ake nema ruwa-a-jallo a Katsina

An hallaka Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari, ƴan ta’addan da ake nema ruwa-a-jallo a Katsina

0
An hallaka Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari, ƴan ta’addan da ake nema ruwa-a-jallo a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, a jiya ta ce ta dakile wani harin da ‘yan ta’adda suka kai musu tare da kashe wasu ƴan ta’adda biyu da ake nema ruwa a jallo.

“An bayyana sunayen ‘yan ta’addan guda biyu da suka shahara da Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari,” in ji kakakin rundunar, Gambo Isah a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Katsina a jiya Talata.

Isah, wanda Sufeto na ‘yan sanda ne, ya ce an kashe ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo ne a lokacin da suka kai hari a unguwar Sokoto Rima da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar.

“A ranar 13 ga Disamba, 2022 da misalin karfe 7:30 na dare, an samu kiran waya cewa ‘yan ta’adda da yawa, suna harbe-harbe da bindigogi kirar AK 47, sun kai hari a Sokoto-Rima Quarters, karamar hukumar Dutsinma, da nufin yin garkuwa da wasu mazauna garin.

“Daga baya, kwamandan yankin Dutsinma da tawagarsa suka yi gaggawar zuwa yankin, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan tare da kashe wasu fitattun ‘yan ta’adda guda biyu a jerin sunayen ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo,” in ji Isah.

Ya kara da cewa an kwato bindigogin AK 47 guda biyu daga hannun su.

Ya kara da cewa, “Jami’an bincike na ci gaba da mamaye wurin da nufin kama wasu ‘yan kungiyar da suka tsere da raunukan harbin bindiga.”