
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Hukumar dake kula da harkokin alhazai a Najeriya (NAHCON) ta ja hankalin mahajjatan da basu dawo daga kasa mai tsarki ba dasu kula da irin kayayyakin da suke dauka domin akwai haramtattun Kayayyaki da hukumomin kula da lafiyar safarar jiragen saman a sararin samaniya suka hana.
Wannan Kiran yazama wajibi a halin yanzu biyo bayan wata ziyarar bazata da jami’ai sukayi a sashin tattara jakakkuna da kayayyakin alhazan inda aka samu mafi yawancin kayayyakin na dauke da haramtattun abubuwa da ka iya zama barazana ga lafiyar matafiya a jirgin saman.
An bukaci mahajjatan da su kara kulawa da kayayyakin dasuke diba kasancewar duk wata jaka da aka samu kayan da aka hana dauka ta hanyar bincike da Na’urar Zamani mai X-ray, toh za’a tsayarda wannan jakar a sashin bincike har sai an kwakwulo abinda ke ciki.
Saboda haka ne ake Jan hankali ga mahajjatan da su kiyaye dibar kayayyakin domin lafiyar su baki daya a jakakkunansu mai nauyin Kturarenlkuma Mai nauyin KG10.
Haramtattun Abubuwan sun hada da turaren kwalba, magungunan kwari, abubuwa masu kunshe da sinadarin gas da kemikal, turaruka masu yawa da dangoginsu dake dauke da sinadaran kamawa da wuta, da sauran kayan dake da alaka da ruwa. Sauran abubuwan da aka haramta sun hada da wuka, reza, dama sauran abubuwa masu kaifi, da bindigogin wasan yara.
Ofishin Shugaban NAHCON ta yi Kira ga mahajjatan dasu kiyaye.
Zuwa yanzu, alhazai 23,727 ne suka samu dawowa Najeriya, harma wasu jahohin sun kammala kwashe alhazan su kaf. Jahohin Oyo, Ogun, Osun, Edo, Kwara, Kogi, Kebbi, Nasarawa, Sakkwato da Kuma tawagar Rundunar Sojojin Najeriya.
Shima jirgin FlyNas, daya daga cikin jiragen da ke kwangilar kwasan alhazan Yana dab da kar-kare kwangilar sa na hajjin bana.