
Gwamnatin tarayya ta umurci dukkan shugabannin manyan asibitocin gwamnatin tarayya da su sayi allura da su rika amfani da allura da da ake ƙera su a gida kuma hukumar NAFDAC ta amince da su.
Sabuwar umarnin na kunshe ne a cikin wata takardar ga dukkan shugabannin asibitoci mai dauke da sa hannun karamin ministan lafiya, Dr Tunji Alausa, a yau Juma’a.
Ministan ya ce an ba da wannan umarnin ne domin bunkasa samar da kayayyakin da ake ƙera wa a cikin gida da kuma kare masana’antun kasar daga kwararar kayayyakin kasashen waje.
Sanarwar ta kuma umarci hukumar ta NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji da aka kera daga kasashen waje.
Alausa ya ce bangaren lafiya ya gano masana’antar harhada magunguna ta cikin gida da ke samar da allura da sirinji wadanda ke cikin matsala matuka saboda wannan mummunar harkar.
Ya kuma ce daga cikin kamfanonin harhada magunguna guda tara na cikin gida da suke samar da allura da sirinji shekaru takwas da suka gabata, shida sun rufe saboda zubar da kayayyakin da ba su da inganci a kasuwa.
“Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa dole ne a daina wannan. Dukkanmu mun amince da daukar matakan da suka dace don magance wannan mummunan yanayi cikin gaggawa.
“A bisa haka, hukumar ta NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji da aka kera daga kasashen waje.
“Haka kuma shine a soke jerin sunayen kamfanonin da ke da hannu wajen shigo da wadannan kayayyakin da ke ci gaba,” in ji shi