
Tsohon mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Mista Doyin Okupe ya bayyana cewar har yanzu Buhari ba shi ne dan takarar Shigabancin Najeriya ba.
Ya bayyana cewar a bisa doka dole ne mutum ya kasance dan Najeriya sannan ya tsaya takarar Shigaban kasa, amma akwai tantamar kasancewar Buhari dan Najeriya, domin dukkan bayanai suna nuna cewar shi dan Sudan ne. A cewar Doyin Okupe.
Okupe ya bayyana hakan ne jiya a Abuja, inda ya Kara da cewar shi kansa Shugaba Buhari ya tabbatar da tantamar kasancewarsa dan Najeriya a jawabansa a kasar Poland.