
Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya ce har yanzu laluben wanda zai yi masa mataimaki a takarar ta sa ya ke.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Abuja, a lokacin kaddamar da wani littafi a bikin cika shekara 60 da haihuwar Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.
Ɗan takarar yana da dama har zuwa ranar 15 ga watan Yuli kamar yadda hukumar zaben kasar ta tanada, ya mika mata sunan wanda zai maye gurbin Kabir Ibrahim Masari, wanda ya bayar da sunansa domin rike wannan mukami na wucin-gadi.
Tinubu, ya yaba wa Shugaban Majalisar Wakilan a kan irin gudummawar da ya ce yana bayarwa ga dumokuradiyya, yana mai cewa abin da ya yi masa a lokacin zaben fitar da gwani abu ne da ba zai iya ambatawa ba a wannan lokaci.
Ya ce, ”Na kashe lokaci mai yawa, lokaci da dama, mutane za su iya kagara, za su iya kyashi, za su iya bakin-ciki ma. Na yi gagarumar nasara, na gode ma.”