Home Wasanni Har yanzu Manchester United tafi kowacce kungiya daraja a Turai

Har yanzu Manchester United tafi kowacce kungiya daraja a Turai

0
Har yanzu Manchester United tafi kowacce kungiya daraja a Turai

Daga Abba Ibrahim Gwale

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sake zama kungiyar da ta fi kowwace daraja a Turai yayin da darajarta ta kai fam biliyan 2,9, in ji kamfanin kasuwanci na KPMG.

Kungiyar ta Ingila ce take kan gaban kungiyoyi ciki har da Real Madrid da Barcelona a nazarin da KPMG ta yi kan darajar manyan kungiyoyin.

Nazarin, wanda aka yi akan kakar wasa ta 2015 zuwa 2016 da kuma kakar wasa ta 2016 zuwa 2017, ya yi duba kan iya samun riba da mallakar hakkin watsa wasanni da farin-jini da nasarar da za ta iya samu nan gaba da kuma darajar filin wasa.

Kungiyar Liverpool da ta kai ga wasan karshe a gasar zakarun Turai tana mataki na shida a cikin jerin sunayen da kamfani ya fitar na kungiyoyi masu daraja.

Daga cikin jerin kungiyoyi 10 na farko da suka fi daraja a Turai cikin 32 da aka yi nazari akansu, akwai kungiyoyin gasar Firimiya shida a sahun farko.

Andrea Sartori, wanda shi ne shugaban sashen wasannin duniya na KPMG kuma wanda ya rubuta rahoton, ya ce darajar harkar kwallon kafa ta karu cikin shekarar da ta gabata.

Ya ce: “jimillar karuwar daraja yana samuwa ne ta dalilai daban-daban, daya daga cikinsu shi ne karuwar kudaden shiga na manyan kungiyoyi 32, wanda ya kai kashi takwas cikin 100.”

“Cinikin musayar ‘yan wasa mai jan hankali da kuma karuwar kudin ma’aikata bai hana wadannan kungiyoyi samun riba ba, yayin da ribar kafin haraji ta karu sau 17 idan aka kwatanta da bara.”