Home Lafiya Har yanzu ba a samu nau’in korona na Omicron a Nijeriya ba- NCDC

Har yanzu ba a samu nau’in korona na Omicron a Nijeriya ba- NCDC

0
Har yanzu ba a samu nau’in korona na Omicron a Nijeriya ba- NCDC

 

Cibiyar yaƙi da cututtuka ta ƙasa, NCDC ta sanar da cewa har yanzu ba a samu nau’in korona na Omicron a ƙasar ba.

Duk da ba a samu nau’in cutar a Nijeriya ba, amma kuma ana ci gaba da samun su a ƙasashe irin su UK, Israel, Botswana, Hong Kong, Germany, Belgium, Italy da sauransu.

Darakta-Janar na NCDC, Ifedayo Adetifa ya baiyana cewa duk da ba a samu rahoton kisa da ga wannan nau’in korona ba, an gano cewa a kwai jinsin ƙwayar har 126 na yawo a faɗin duniya wanda a ka wallafa a wata mujallar tattara bayanan korona na duniya.

Adetifa ya ƙara da cewa Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasa da NCDC na sane kuma suna zura ido a kan sabon nau’in cutar na korona, in da ya ce tuni Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta aiyana shi a wani nau’i mai ban tsoro ta kuma raɗa masa suna da Omicron.

“Gwamnatin tarayya ta ƙara ƙarfafa sa ido a filayen jirgin sama da sauran gurare sannan ta kafar dokar yin gwajin korona na dole a waɗan nan guraren domin tabbatar da bin matakan kariya na tafiye-tafiye da Hukumomin lafiya su ka gindaya,” in ji Darekta-Janar ɗin.

 

Daily Nigerian Hausa