
Babban Bankin bayar da lamuni na duniya IMF ya fitar da wata sanarwa ranar Juma’a, inda yace har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana cikin matsanancin yanayi, duk kuwa da cewar a hukumance an bayar da sanarwar fita daga cikin halin matsin tattalin arzikin da aka shiga a najeriyar.
A sanarwar da IMF ta bayar ta hannun jami’in hulda da jama’a na Bankin, Rapheal Ranspach, yace aniyar gwamnatin Najeriya na yin hobbasa akan inganta sha’anin wutar lantaki abin a yaba ne ainun, domin hakan wani yunkuri ne na mayar da hankali wajen farfado da harkokin kasuwancin kasar.
Dole ne Najeriya ta yi shiri na musamman kan batun samun kudin shigarta na gamayya, da kuma yadda tattalin arziki zai samu bunkasa ta hanyar taimakawa sassan kasuwanci masu zaman kansu, wanda suke taimakawa wajen juya tattalin arzikin kasar ya kai zuwa ga mutane na kasa.
Bankin bayar da lamuninya turo wata kakkarfar tawagar kwararru zuwa Najeriya karkashin jagorancin AMine Mati, daga ranar 6 ga watan Disamba zuwa 20 ga watan a wannan shekarar ta 2017, domin bibiya tare da yin nazari kan kasafin kudin Najeriyar na shekarar badi mai kamawa, wanda wancan bin diddigi ya kai ga samar da wannan rahoto.
“Ba shakka, a hukumance Najeriya ta bayar da sanarwar fita daga halin matsin tattalin arziki, amma zance na zahiri shi ne, tattalin arzikin Najeriya na cikin garari, domin kuwa yana tafiyar wahainiya ne. Domin kuwa, muwalitin kasafin kudin wannan shekarar ya karu ne da 1.4 a rubu’in wannan shekarar me karewa, wannan kuwa ba wani bayani bane mai karfafa guiwa kan batun tattalin arzikin Najeriyar. ita ma wannan farfadowar sashin man Najeriya da kuma sashin Noma da kasar ta mayar da hankali akai, sun taimaka ba da wani abu na kuzo mu gani ba”
“Haka kuma, wasu sassa daban da ba na Mai ko sashin Noma bane, suka taimakawa wajen samar da bunkasar wasu sassan tattalin arzikin Najeriyar da ya kai kashi 65, a rubu’in farko na wannan shekarar, abinda farko ya nuna kamar za’a yi wani abin kirki, kafin daga bisani alkaluma su sauya”
“Kakanikayin da harkar kudi take ciki, ta taimaka wajen samar karuwar hauhawar farashi da kayayyaki suke yi, wannan yasa kamfanoni ba su da wani zabi na samun bunkasa, ko kuma bukatar masu nema”
A dan haka ne, IMF ta shawarci Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye ta zage dantse domin fuskantar da alkiblar tattalin arzikin Najeriya zuwa ga wani yanayi da zai sanya nutsuwa da kuma farinciki dangane da tafiyar tattalin arzikin.
Dole ne Gwamnatin Najeriya ta yi dukkan wani shiri da zai kai ga samuwar daidaitar farashi, da kuma, sanya nutsuwa ba tare da garari ba a tare da ‘yan kasuwa masu zuba jari daga ketare.