
Rundunar Ƴan Sanda ta Babban Birnin Nijeriya, Abuja ta ce ta kama mutane 4 da kuma tsare motoci 21 sakamakon laifin yin haramtaccen tseren mota da sauran laifuka makamantan hakan.
Kakakin rundunar, DSP Josephine Adeh ce ta baiyana haka a yau Litinin a Abuja.
Ta ce an kama waɗanda a ke zargi ɗin ne, sannan da tsare motocin a bisa dogaro ga sashi na 228 na dokokin kula da tituna wanda ya hana yin tseren mota ba tare da izini ba.
Ta ƙara da cewa gungun ƴan sandan sintiri ne, a bisa jagorancin Kwamishinan Ƴan Sanda na Abuja, Babaji Sunday su ka yi kamen da tsare motocin a jiya Lahadi.
Kakakin ta ƙara da cewa an kama masu laifin ne a titin Muhammadu Buhari, daidai Nicon Inshora inda su ka saba yin tseren.