Home Kasuwanci Haramun ne a yanke wa mutum wuta ba tare da bashi sanarwar kwanaki 10 ba — Gwamnati

Haramun ne a yanke wa mutum wuta ba tare da bashi sanarwar kwanaki 10 ba — Gwamnati

0
Haramun ne a yanke wa mutum wuta ba tare da bashi sanarwar kwanaki 10 ba — Gwamnati

 

 

 

 

Hukumar Kare Mai saye da Mai sayarwa ta Tarayya, FCCPC, ta ce haramun ne a yanke wa mutum wuta ba tare da bashi sanarwa ta kwanaki goma da ga ranar da a ka aiko masa da takardar biyan kuɗi ba.

Babatunde Irukera, Mataimakin Shugaban Hukumar ne ya bayyana haka a jiya Laraba a Calabar, a wani dandalin warware korafe-korafen masu amfani da wutar lantarki.

Irukera ya koka da yadda Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Fatakwal, PHED, ke yi a Calabar da kewaye.

Ya ce daga binciken da hukumar ta yi, PHED ba ta yi wani abin azo a gani ba wajen samar da wuta ga al’umma daidai da kudaden da kamfanin ya caje su ba.

Hakan ne ya sanya Irukera ay ayyana ayyukan kamfanin rarraba wutar lantarki na Cross Rivera a matsayin “zalunci”.

Ya ce rahotannin da suka samu kan al’amura da dama sun hada da yanke wa jama’a wuta da kamfanin ke yi ba tare da bin doka ba.

“Yawan yanke wutar al’umma saboda bashi ba wai kawai bisa ka’ida ba ne, abin takaici ne da kuma cin zarafin jama’a. Yanke wa al’umma wuta ba bisa ka’ida ba zalunci ne,” in ji shi.