Home Labarai Hare-haren ƴan IPOB a Imo yana damu na — Buhari

Hare-haren ƴan IPOB a Imo yana damu na — Buhari

0
Hare-haren ƴan IPOB a Imo yana damu na — Buhari

 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa a bisa hare-haren ƴan haramtacciyar ƙungiyar masu rajin samar da yankin Biafra, IPOB.

A tuna cewa a ranar Asabar ne dai ƴan IPOB su ka kai hari gidan Shugaban Ohaneze Ndigbo, Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, a Awo-Omanma, Ƙaramar Hukumar Oru ta kudu.

A wata sanarwar da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar Lahadi a Abuja, Buhari ya yi alla-wadai da harin, inda ya yi kira ga a zauna lafiya.

A cewar sa, a na nan a na duba da gyara yanayin doka da oda a shiyyar Kudu-maso-Gabas.

Shi yasa Buhari ya yi kira ga al’ummar Jihar Imo, musamman, da kuma na shiyyar gaba daya da su zauna lafiya domin yan sanda na kai-komo don samar da zaman lafiya.

Buhari ya jajanta wa ƴan sanda bisa rashin jami’ai Da kayan aiki da su ka yi, inda ya kuma jajanta wa Obiozor , wanda ya yi kira gare shi da ya ci gaba da aikin sa na samar da zaman lafiya da haɗin kai.