Home Labarai Hari a kan mamba: Masu sayar da tumatur, kayan abinci da shanu sun yi barazanar dena kai kaya Legas

Hari a kan mamba: Masu sayar da tumatur, kayan abinci da shanu sun yi barazanar dena kai kaya Legas

0
Hari a kan mamba: Masu sayar da tumatur, kayan abinci da shanu sun yi barazanar dena kai kaya Legas

Kungiyar dillalan tumatir ta Najeriya da hadaddiyar kungiyar dillalan abinci da shanu ta Najeriya sun yi barazanar katse kai kaya zuwa jihar Legas tumatur bisa zargin lalata musu kayayyaki da wasu ɓatagari su ka yi a jihar.

Shugaban kungiyar dillalan tumatur ta kasa, Ahmed Alaramma ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Zariya a jiya Lahadi.

A cewarsa, harin da aka kai kan ‘ya’yan kungiyar a kasuwar Oke-Odo da ke Legas a kwanakin baya ya yi sanadiyar lalata tumatur na sama da Naira miliyan 360.

“Sama da mambobin kungiyar 70 ne ke ba da hayar mazubi ga dillalan tumatur a fadin kasar nan; muna da mazubi sama da dubu 60,000 da ake shirin mayar da su arewa a lokacin tashin hankalin.

“Yanzu kuma ɓatagari sun kone mazuban nan a yayin rikicin kuma suka hana yaran mu su kashe wutar muna da shaidu a kan haka,”in ji shi

Ya ce an kone musu mazubai da owannennsu ya kai Naira 6,000, jimilla ta yi asarar jarin N360m.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya, da gwamnatin jihar Legas, da sauran masu ruwa da tsaki da su duba asarar da aka yi tare da biyan kungiyar diyya.