Home Labarai Harin gidan yarin Kuje: Fursunoni 4 sun mutu, 16 sun jikkata yayin da 879 suka tsere – NCoS

Harin gidan yarin Kuje: Fursunoni 4 sun mutu, 16 sun jikkata yayin da 879 suka tsere – NCoS

0
Harin gidan yarin Kuje: Fursunoni 4 sun mutu, 16 sun jikkata yayin da 879 suka tsere – NCoS

 

 

Hukumar kula da Gidajen yari ta Ƙasa, NCoS ta ce fursunoni huɗu na gidan yari na Kuje sun mutu yayin da 879 suka tsere a harin da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Abuja.

Umar ya ce maharan sun kutsa cikin gidan yarin ne da ke Kuje, inda suka yi amfani da gurneti su ka ɓalle babbar kofar shiga da kuma ta katanga.

Ya ce an kashe jami’in hukumar tsaron fariren hula ta ƙasa, NSCDC da ke tsaron gidan yarin, inda ya ce jami’an NCoS uku sun samu munanan raunuka.

“Jimillar fursunoni 879 ne suka tsere daga wurin a lokacin da aka kai harin. Ya zuwa wannan rahoto, an sake kama mutane 443, fursunoni 551 a halin yanzu suna tsare, fursunoni 443 na hannunsu.

“ Fursunoni hudu sun mutu sannan 16 sun samu raunuka daban-daban kuma ana kula da su a halin yanzu. Sai dai ana ci gaba da kokarin kamo dukkan fursunonin da suka gudu,” inji shi.