Home Labarai Harin gidan yarin Kuje: Buhari ya kira shugabannin hukumomin tsaro

Harin gidan yarin Kuje: Buhari ya kira shugabannin hukumomin tsaro

0
Harin gidan yarin Kuje: Buhari ya kira shugabannin hukumomin tsaro

 

 

 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Ƙasa tare da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo da wasu ministocin majalisar ministoci da dukkan shugabannin tsaro.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa sauran da su ka halarci taron tsaron sun haɗa da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sai dai kuma Babban Hafsan Sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo ya samu wakilci a taron.

NAN ta samu labarin cewa a taron, za a tattauna ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta sakamakon harin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a Gidan Yarin Kuje, inda manyan fursunonin Boko Haram suka tsere.