
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sake ba da umarnin a kuɓutar da sauran fasinjojin jirgin ƙasa da aka yi garkuwa da su da ransu.
Shugaban ya ba da umarnin ne a yau Talata a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar a Abuja.
A cewar Garba Shehu, sojoji da hukumomin tsaro na ƙasa sun san nauyin da ke kansu na al’ummar kasar kuma sun kuduri aniyar cika umarnin da shugaban ya yi cikin gaggawa.
Shehu ya ce shugaban kasar ya ba da umarnin kara ƙaimi da ya haɗa da mataki na amfani da ƙarfi da kuma na maslaha domin kawo karshen batun cikin gaggawa.
“Bayan amincewar shugaban ƙasa, gwamnati na ci gaba da bin hanyoyi biyu, na ƙarfi da na maslaha don tabbatar da sakin fasinjojin cikin koshin lafiya.
“Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a sako ‘ya’yansu, kuma bayan an sasanta lamarin, sai suka saki goma sha ɗaya daga cikin waɗanda su ka kama, duk da cewa mun tsammaci za su saki dukkanin su.
“Amma duk da haka, gwamnatin ba za ta gaza ba wajen ganin an kuɓutar da duk waɗanda a ka yi garkuwa da su,” in ji shi