
Wasu fasinjoji da su ka tsira da ga mummunan harin da ƴan ta’adda su ka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja-Kaduna ranar Litinin, sun yaba wa sojoji da su ka kawo musu ɗauki a lokacin harin.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa mutane 8 ne su rasu, 26 su ka samu raunuka a harin, inda ƴan ta’addan su ka yi awon-gaba da wasu da ga cikin fasinjojin.
A wata hira ta wayar salula da ya yi da wakilin VOA Hausa, Nasir El-Hikaya, wani fasinja da ya tsira da ransa, Shu’aibu Adamu Alhassan ya ce harin ya ƙazanta.
A hirar, wacce ta karaɗe kafofin sadarwa, Alhassan ya ce bai taɓa shiga halin tashin hankali irin wannan ba.
A cewar sa, bayan ƴan ta’addan sun kwashe sama da awa ɗaya su na cin karen su ba babbaka a jirgin, can sai ga sojoji a motoci sama da 30, inda su ma su ka budewa ƴan ta’addan wuta su ka kore su da ga wajen jirgin.
Ya ƙara da cewa bayan sojojin sun zo ne su ka riƙa sanarwa cewa kowa ya kwantar da hankalinsa, inda su ka riƙa fito da mutane, wadanda su ka rasu da wandanda su ka samu raunuka.
Alhassan ya ƙara da cewa har goya waɗanda ba za su iya tafiya ba sakamakon raunuka sojojin su ka riƙa yi, inda ya ƙara da cewa sojojin sun maida jikinsu matakala domin samar wa mutane wajen zama a kan tsauni kafin a kawo motocin da za su kwashe su.
Alhassan ya yi kira da al’umma da su yi wa sojojin addu’a domin samun nasara a kan ƴan ta’adda, inda ya ce su na iya bakin ƙoƙarin su wajen kare ƙasar nan.
Ita ma Maimuna Ibrahim, wacce a ka harba a cinya, ta shaida wa jaridar The Cable cewa wani soja ne ya goya ta sabo da ta kasa tafiya.
Ta tabbatar da cewa sojojin sun yi kokari matuƙa kuma su na bukatar addu’a da goyon baya da ga ƴan ƙasa.