
An bayar da rahotannin akalla mutane 4 ne suka rasu yayin da wasu 8 suka samu munanan raunuka a sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci a yankin karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar, an kai wannan hari ne makonnin hudu bayan da dubban mutane suka koma gidajensu a garin sakamakon zaman lafiya da ya dan dawo yankin.
Shugaban karamar hukumar Bama, Baba-Shehu Gulumba, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, cewar mutane hudu sun mutu a harin da aka kai wani masallaci da Asubah.
Shugaban ya bayyana cewar, wasu yara da suka hada da mace da namiji ne guda biyu suka layyace jikinsu da bamabamai, suka kuma kutsa kai cikin masallacin dake rukunin gidajen Bama-Dina, sannan suka tayar da Bom din da ke jikinsu.
Ya kara da cewar, lamarin ya auku da misalin karfe biyar na asubahi, yayin da mutane suka fito Sallar Asubah.
Ya kuma tabbatar da cewar, mutane uku sun rasu nan take, yayin da guda ya cika bayan da aka garzaya da shi asibiti a birnin Maiduguri, ya kara da cewar, wadan da suka samu raunuka suma an wuce da su zuwa asibiti a Maiduguri domin basu kulawa ta gaggawa.
Ya cigaba da cewar, daman dai tni Gwamnatin jihar ta tura karin jami’an tsaron sojoji da ‘yan sanda zuwa yankin domin kula da shige da ficen mutane a yankin, bayan da dubban mutanan Bama suka koma gida daga hijirar da suka yayi yayin da hare hare suka yi tsanani a yankin.
Yace “Mun takaita zirga zirgar mutane daga karfe shida na yamma zuwa safiya a yankin, sannan kuma ana neman mutane su bayar da hadin kai”
Shugaban karamar hukumar ya kuma tabbatar da burinsu na tsayawa dmin baiwa al’umma cikakkiyar kulawa, dan ganin irin hakan bata sake aukuwa ba a yankin.
NAN