Home Labarai HASASHE: Nijeriya za ta zarta Amurka a yawan al’umma 

HASASHE: Nijeriya za ta zarta Amurka a yawan al’umma 

0
HASASHE: Nijeriya za ta zarta Amurka a yawan al’umma 

 

 

Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya yi hasashen cewa Najeriya za ta zama kasa ta uku a yawan al’uma a duniya kafin shekarar 2050.

Binciken ya nuna cewa Nijeriya za ta zarta Amurka a yawan al’umma kafin shekarar ta 2050.

Haka kuma an yi hasashen cewa zuwa watan Nuwamban 2022 yawan al’umar duniya zai kai kusan biliyan takwas.

Binciken ya kuma nuna cewa yawan al’umar Indiya zai zarta na China a shakarar 2023

A yanzu dai yawan al’umar duniya ya kai biliyan 7.6, ana kuma hasashen zai kai biliyan 8.6 a 2030, sai biliyan 9.8 a shekarar 2050, sannan ya kai biliyan 11.2 a shekarar 2100.