
Rahotanni sun baiyana cewa Ƴan Sanda sun harba hayaƙi mai yaji kan wakilai da a ka tantance da ma ƴan jarida a filin taron na Eagle Square da ke Abuja.
Hatsaniya ta faru ne lokacin da ƴan daba su ka danno wajen taron inda su ke ƙoƙarin banƙara mashigar wajen taron.
Lamarin ne ya tilasta wa jami’an tsaro su harba hayaƙi mai yaji, inda wakilai masu zaɓe da ƴan jarida su ka ranta a na kare domin tsira.
Hakan ne ya baiwa ƴan daban damar yin sane, inda su ka sace wayoyi da kuɗaɗen wasu da ga cikin wakilai da ƴan jarida.
Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa an kama da yawa da ga cikin ƴan daban.