Home Kasuwanci Hauhawar farashi ya karu da kashi 20.77 a Nijeriya

Hauhawar farashi ya karu da kashi 20.77 a Nijeriya

0
Hauhawar farashi ya karu da kashi 20.77 a Nijeriya

 

Hauhawar farashi ta yi tashin gwauron zabo da kashi 20, inda ake samun karuwar tsadar kayan abinci da makamashi da kuma ci gaba da faduwar darajar kudin naira.

Alkaluman hukumar kididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashin ya tashi zuwa kashi 20.77 a watan Satumba daga kashi 20.52 da yake a watan Agusta, wanda ba a taba ganin irin sa ba tun shekarar 2005.

Kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo zuwa kashi 23.4, idan aka kwatanta da kashi 23.1 da yake a watan Agusta.

Ana kuma ganin cewa matsin lamba zai iya sanya kwamitin tsare-tsare mai kula da kudi na Babban Bankin Najeriya ya kara yawan bashi da yake ciyowa a karo na hudu a jere a watan Nuwamba.