Home Siyasa Hayatu-Deen ya janye daga takarar shugaban kasa, inda yai alkawarin marawa PDP baya

Hayatu-Deen ya janye daga takarar shugaban kasa, inda yai alkawarin marawa PDP baya

0
Hayatu-Deen ya janye daga takarar shugaban kasa, inda yai alkawarin marawa PDP baya

 

 

 

Mohammed Hayatu-Deen, ɗan takarar zama shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya janye daga takarar.

A yau Asabar ne aka shirya gudanar da babban taron jam’iyyar PDP na musamman, inda ake sa ran wakilan zaɓe za su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023.

Tsohon Manajan-Darakta na rusasshen bankin FSB, ya bayyana janyewarsa daga takarar ne a wata wasiƙa da ya aike wa Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Yayin da ya ke bayyana dalilansa na janye takarar, Hayatu-Deen ya ce ” harkar kuɗi ce ƙarara”.

Sai dai kuma ya yi alƙawarin cewa zai bada gudunmawa da goyon bayan sosai wajen ganin PDP ta samu nasara a babban zaɓen 2023.

“A ƙarshe, a matsayina na amintaccen ɗan jam’iyya kuma mai bin tsarin dimokuradiyya, zan ci gaba da shiga harkokin jam’iyya da ni da ɗumbin magoya bayana a kowane lokaci don ganin nasarar babbar jam’iyyarmu,” in ji shi.