Home Labarai Hisbah ta kama ɓata-gari 23 a Kano

Hisbah ta kama ɓata-gari 23 a Kano

0
Hisbah ta kama ɓata-gari 23 a Kano

 

 

A daren jiya Talata ne dakarun hukumar Hisbah a jihar Kano su ka kai sumame a gidajen 3 da ake zargi, samari da ƴan mata kan hadu su na aikata masha’a

Tun da fari, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dr Harun Muhammad Sani Ibn sina yace maƙwabtan waɗannan gidaje da ake zargi su ne su ka kaiwa hukumar korafi, a lokuta daban-daban, tare da nuna takaicin yadda ake barin ƙananan yara shiga irin wancan gida.

A lokacin sumamen an sami nasarar cafke matasa 23 da su ka haɗa da maza 4 da kuma ƴan mata 19 a lokacin da suke tsaka da aikata rashin tarbiyya.

Da isar su wajen, dakarun Hisbah ba su yi wata-wata ba su ka daka musu wawaso, inda su ka kwashe su izuwa shalkwatar hukumar ta Hisbah.

Bincinken da dakarun Hisbah na farin kaya su ka gabatar, ya tabbatar da cewa ana shan shisha da sauran kayan maye, baya ga aikata baɗala a gidan.

Wuraren da aka kamo matasan sun hadar da Tukur road a unguwar nasarawa, Sultan road, shi ma a unguwar nasarawa, da Kuma zuwa asibitin Nasarawa wato Hospital road.

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar Lawan Ibrahim fagge ya fitar a yau Laraba a Kano, ya ce Ibn Sina ya yi tsokaci, inda ya ba da tababbacin cigaba da kai sumame har ma da ɗaukan matakan shari’a a kan irin waɗannan gidajen.

Sannan ya gargadi iyaye tare da Jan kunnen matasa da su guji jefa kan su cikin aiyukan masha’a domin samun shuwagabani na gari.