
Rundunar Hisbah a Jihar Jigawa ta kama jarkoki 8 masu yawan lita 25 maƙare da barasar gargajiya da a ke kira da Burkutu.
Rundunar ta yi kamen ne a Ƙaramar Hukumar Maigatari a jiya Talata, inda ta kuma kama kwalabe 96 na giyar zamani.
Kwamandan Hisbah na Jigawa, Ibrahim Dahiru, shine ya shaidawa NAN labarin lamarin a Dutse.
Ya ce jami’an Hisbah ne su kankama kayan mayen da misalin ƙarfe 3:30 na dare lokacin sun kai sunane wani waje da ake kuma cin nama barkatai.
Ya ce an kama kayan ne da ga wajen mai gurin mai suna Garba Bakule.
Dahiru ya ce tuni rundunar ta miƙa wanda ta kama ɗin ga ƴan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace.