Home Labarai Hisbah ta kama namiji da mace su na lalata a tashar mota a Zamfara

Hisbah ta kama namiji da mace su na lalata a tashar mota a Zamfara

0
Hisbah ta kama namiji da mace su na lalata a tashar mota a Zamfara

 

Jami’an Hisbah a Jihar Zamfara sun kama wasu mace da namiji waɗanda ake zarginsu da lalata a tsakiyar wata tashar mota da ke birnin Gusau na Jihar Zamfara.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa waɗanda ake zargin sun yi lalatar ne tsirara ba tare da la’akari da wani na kallon su ba.

Sakamakon haka ne jama’ar da ke tashar motar su ka yi sauri su ka sanar da jami’an Hisbah, waɗanda a cikin gaggawa su ka isa tashar suka yi awon gaba da su.

Waɗanda su ka shaida lamarin sun ce lamarin ya faru ne bayan namijin ya ƙalubalanci matar kan cewa ya fi ta rashin kunya, inda ita ma ta ƙalubalance shi cewa ta fishi fitsara, wanda daga nan suka soma wannan aika-aika.

Tuni dai aka gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Kankuri da ke garin Gusau.

A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa, an nuna waɗanda ake zargin, inda namijin da ake zargi ya ce bai san yadda aka yi hakan ta faru ba.

A cewarsa,tun a farko ya je wurin wani biki ne inda daga nan ne ya ke kyautata zaton aka ba shi wani abu na maye ya sha.

Ita kuwa macen cewa ta yi wannan abin ba halinta bane, inda ta ce hasali ma sana’ar sayar da sanduna take yi.

Ta bayyana cewa idan ba ta samu cinikin sandunan bane ta ke shiga wannan hali.