Home Labarai Hisbah ta shawarci ma’aurata da su yi gwajin lafiya kafin aure a Kano

Hisbah ta shawarci ma’aurata da su yi gwajin lafiya kafin aure a Kano

0
Hisbah ta shawarci ma’aurata da su yi gwajin lafiya kafin aure a Kano

 

 

 

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta shawarci ma’aurata da su san yanayin lafiyar abokan zamansu kafin su yi aure domin daƙile yaɗuwar cutar ƙanjamau.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya fitar a Kano.

Ibrahim Fagge ya bayyana cewa, mukaddashin kwamandan hukumar, Hussain Ahmad ne ya bayyana haka a lokacin da ya tarbi jagorancin kungiyar Achievers Improved Health Initiatives, AIHI, a shelkwatar hukumar da ke unguwar Sharada.

Ya nakalto mukaddashin kwamandan na tabbatar da cewa, hukumar za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga yunkurin da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi na inganta lafiyar jama’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Hisbah za ta hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin kara wayar da kan jama’a kan illar cutar kanjamau.

“Wannan ko shakka babu zai shawo kan yaduwar kwayar cutar da sauran cututtuka masu yaduwa a tsakanin jama’a,” in ji shi.

Tun da fari, kakakin AIHI, Ibrahim Hassan, ya ce sun kai ziyarar ne domin karfafa alakar aiki tsakanin kungiyoyin biyu domin amfanin jama’a.