
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama katan 18 na barasa a wani shago dake titin Sultan Road a yankin Nasarawa GRA.
Mukaddashin shugaban hukumar, Malam Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikowa DAILY NIGERIAN HAUSA a yau Laraba.
Ya kara da cewa hukumar ta kai samame wasu gidaje da ake zargin ana ta’ammali da miyagun kwayoyi inda aka samu kayan maye tare da kama maza 9 da mata 3.
“Cikin taimakon Allah, Operation ‘Ba Barasa’ sun tafi Operation kuma Allah ya basu nasara, wanda suka yi kokari suka samo wadannan gidaje da muke kuka da su a can bayan rukunin gidajen Kwnakwasiyya. Wanda gida ne zaka gani an mayar da shi Logging, ga mata ga maza, ana ta masha’a . Alhamdulillah, sun samo mata wajen guda tara maza guda 3”, inji Malam Mujahid.
Mukaddashin shugaban hukumar, ya ce kofarsu a bude take ga mutanen wajen su zo su sanar dasu duk inda suke zargin ana aikata ba daidai ba domin daukar mataki.
Sannan ya godewa al’umma bisa hadin kan da suke basu wajen kawar da ayyukan alfasha a jihar ta Kano.