
Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta ƙwace kwalabe 1,906 na barasa iri-iri a sintiri daban-daban da ta gudanar a jihar a 2021.
Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru ya baiyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Dutse a yau Talata.
Dahiru ya ce an ƙwace waɗannan kayan mayen ne a lokacin da jami’an Hisbah su ka kai samame a wuraren shaye-shaye da otal-otal da ke jihar.
Ya ce an kama waɗanda a ke zargi da karuwanci su 92, inda ya ce an damƙe su ne sakamakon aikata baɗala.
“An kama waɗanda ake zargin da aikata lalata da suka hada da caca, karuwanci na shirya raye-raye a lokacin bukukuwan aure da sauransu.
“Har ila yau, hukumar ta samu damar rufe gidajen karuwai a fadin jihar a cikin lokacin da ake nazari,” in ji shi.
Dahiru, wanda ya nanata cewa an haramta shan barasa a tsakanin musulmi masu kishin jihar, ya kuma bukaci mazauna jihar da su guji aikata ayyukan lalata da sauran munanan dabi’u da ke iya lalata al’umma.
Ya kuma ƙara da cewa, an miƙa su ga ‘yan sanda wadanda aka kwace da kuma wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ci gaba da daukar mataki.