Home Lafiya Hukuma a Amurka ta baiwa asibitocin Nijeriya 3 masu zaman kansu tallafin dala miliyan 3

Hukuma a Amurka ta baiwa asibitocin Nijeriya 3 masu zaman kansu tallafin dala miliyan 3

0
Hukuma a Amurka ta baiwa asibitocin Nijeriya 3 masu zaman kansu tallafin dala miliyan 3

 

 

Hukumar Ciniki da Ci-gaban Amurka, USTDA, ta ba da tallafin dala miliyan uku ga wasu asibitoci masu zaman kansu guda uku a Nijeriya don inganta harkokin kiwon lafiya.

Daraktan, USTDA, Enoh Ebong, wacce ta bayyana hakan a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja a jiya Litinin, ya ce sama da ƴan Nijeriya dubu 25 ne za su ci gajiyar tallafin.

Ta jera asibitocin da za su amfana kamar: Lily Hospitals Ltd., Cedarcrest Hospital, da Mobihealthcare Limited (Mobihealth).

Ms Ebong ta bayyana cewa manufar aikin ita ce samar da ingantaccen kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya ta hanyar hadin gwiwa da ma’aikatan lafiya.

A cewarta, aikin ya kunshi samar da kudade tare da saka hannun jari mai ma’ana ta hanyar tallafin da zai bude hanyoyin lamuni da kuma yadda za a aiwatar da su.

An bada tallafin ga Lily Hospitals Limited ne don yin nazari da bincike kan yiwuwar tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya 10 a Nijeriya.

Waɗannan wuraren, waɗanda ke cikin cibiyoyin birane da yawa a duk faɗin ƙasar, za su yi hidimar marasa lafiya har 25,000 kowace shekara.

Ta ce Lily ta zaɓi ƙungiyar Anadach Consulting Group, LLC, mai tushen Maryland don gudanar da binciken.

Ms Ebong ta yabawa asibitocin Lily saboda farfado da asibitocin da suke cikin mummunan yanayi domin amfanin ‘yan Najeriya.