
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci ta Jihar Kano, PCACC, ta kama wani Darakta, Bello Alkarya, na Hukumar Kula da Ingancin Kayaiyaki ta jiha, bisa zargin karɓar na-goro.
Jaridar Daily Trust ta baiyana cewa Shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci ɗin na riƙon ƙwarya, Barista Mahmud Balarabe, ya ce an kama Alkarya, wanda a ka fi sani da Nijeriya, a yayin da ya ke karɓar na-goro.
“yanzu haka mun cafke shi lokacin da yanke karɓar. Yanzu haka yana ofishin mu mun saka shi a dakin ajiye masu laifi. Muna nan muna bincike,” in ji Balarabe.
Jaridar ta rawaito cewa a baya ma an kama wani Darakta da karɓar na-goro a hukumar.