
Hukamar da ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa da almundahana ta kasa EFCC ta fara bincikar tsohon Shugaban majalisar Dattawa Sanata David Mark bisa zargin bacewar makudan kudade lokacin Shugabancinsa.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewar, a daren jiya tsohon Shugaban majalisar Dattawa Sanata David Mark ya halarci shalkwatar hukumar EFCC a Abuja, inda ake tuhumarsa da bacewar biliyoyin kudaden da aka ware domin ayyukan raya mazabun ‘yan majalisar dattawa tsakaninsa da wasu shafaffu da mai a majalisar.
Hukumar ta amince Sanata David Marka ya koma gida tun a daren jiyabayan da akai masa tambayoyi, tare da yarjejeniyar zai dawo bayan kammala bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar Shekara.