Home Labarai Hukumar Hadeja-Jama’are ta ƙaryata rahotannin ɓallewar dam ɗin Tiga

Hukumar Hadeja-Jama’are ta ƙaryata rahotannin ɓallewar dam ɗin Tiga

0
Hukumar Hadeja-Jama’are ta ƙaryata rahotannin ɓallewar dam ɗin Tiga

 

 

 

Hukumar raya kogunan Hadeja -Jama’are ta ƙaryata wasu hotanni da hotuna da ake yaɗa wa cewa dam ɗin Tiga da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji a Jihar Kano ya ɓalle.

Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na hukumar, kuma sakataren harkokin Mulki Salisu Baba Hamza ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a nan Kano.

Sanarwar ta ce tun farkon watan Agusta ruwan kogin ya fara fita kuma har yanzu ruwan yabna cigaba da fita ta hanyar da aka tsara masa ya fita domin rage yawansa.

Hukumar ta ce sakamakon mamakon ruwan sama a jahohin Kaduna da Plateau, dam ɗin ya kara tumbatsa kuma fitar ruwan ta karu daga kogin.

Hamza ya ƙara da cewa “kar a manta wannan lokaci ne na damina kuma mu na cikin watanni da ake samun mamakon ruwan sama, sannan dama hukumar kula da yanayi ta Najeriya tayi hasashen fuskantar ruwa da yawa a sassan wannan kasa.

“Kogunan dake karkashin hukumar raya kogunan Hadeja Jama’are basu taba samun kulawa kamar a irin wannan lokaci ba musamman bayan kammala ayyukan gyara madatsun ruwa domin inganta noman rani na TRIMMING, haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar ruwa ta tarayya da bankin duniya.

“Wannan hukumar ta Hadeja Jama’are tana kira ga masu makwaftaka da kogin su rika bada rahoton duk wani bakon abu da suka gani a dam din na Tiga yayinda hukumar ke bada tabbacin aminci da kariya daga tsarin kulawa da kogin,” in ji shi.