Home Labarai Hukumar Hajji ta Uganda ta buƙaci maniyyata su ajiye kashi 70 na kuɗin Hajji

Hukumar Hajji ta Uganda ta buƙaci maniyyata su ajiye kashi 70 na kuɗin Hajji

0
Hukumar Hajji ta Uganda ta buƙaci maniyyata su ajiye kashi 70 na kuɗin Hajji

Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Uganda ta fitar da wani cikakken tsari domin taimakawa musulmin da ke da sha’awar zuwa aikin Hajji a shekarar 2024.

Wani bangare na shirin da aka fitar shi ne na ajiye kashi 75 cikin 100 na abin da su ka biya a 2023.

An bayyana shirin ne na ko-ta-kwana ga tsauraran sabbin ka’idoji da gwamnatin Saudiyya ta ɓullo da su ga maniyyata aikin hajjin 2024 zuwa Madina da Makka.

Babban Sakatare Janar na Ofishin, Sheikh Twaib Bogere ya ce an fara rajistar maniyyata cikin gaggawa tare da hadin gwiwar kamfanoni daban-daban.