
Hukumar lura da hakkin Da-Adam ta kasa, NHRC, shiyyar Arewa maso yamma, a babban ofoshinta dake Kano, ta bayyana cewar a shekarar bara ta samu korafe korafe kusan 583, sannan kuma taci nasarar horas da ‘yan sanda 50 kan yadda zasu kare ‘yancin al’umma.
Babban kodinetan hukumar shiyyar Arewa maso yamma, Hajiya Hauwau Salihu ce ta bayyana haka a Kano, inda tace a cikin kararraki 583 da hukumar ta karba, 256 an bibiyesu kuma an kai karshensu, sauran 327 sune har yanzu ake bibiya.
Ta bayyana cewar, mafiya yawancin koken da hukumar take samu, batu ne da ya shafi mutanen a gidajensu da unguwanninsu. Da kuma batun ciyarwa bayan miji ya rabu da matarsa ga yaran da suka haifa.
Hajiya Hauwa ta cigaba da cewa, sauran korafe korafen sun hada da, batun gado, tsare mutane ba da hakki ba, cin zali, tursasawa, da kuma azabtar da yara ba are da wani hakki ba.
Kodinetan hukumar, ta bayyana cewar galibin kararrakin da ke wajensu, suna bukatar sasantawa ne da kuma tattaunawa domin gano bakin zarensu.
Sannan kuma tace, wasu korafe korafen suna mika su ne zuwa kotuna domin samun maslaha a can domin gudanar da zuzzurfan bincike kan wasu matsalolin.
Haka kuma, ta kara da cewar hukumar ta kammala duk wasu shirye shirye na baiwa wasu karin ‘yan sanda guda 50 horo a wannan shekarar ta 2018.