Home Bayani Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara harajin Naira biliyan 300 a shekarar 2017

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara harajin Naira biliyan 300 a shekarar 2017

0
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara harajin Naira biliyan 300 a shekarar 2017
Hadiza Bala usman, Shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeeriya NPA

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara harajin Naira biliyan 299.5 a shekarar 2017 da ta gabata. Babban Kwamishinan sadarwa na hukumar Abdullahi Goje shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar talata a Legas.

Kwamishinan yace, alkalun sun zarta abinda aka samu a shekarar 2016 da kaso 84.65.

Mista Goje ya cigaba da cewar, wannan shi ne karon farko cikin shekaru biyar da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta tara wannan zunzurutun makudan kudade a shekarar 2017.

“A shekarar 2013, hukumar a tara Naira biliyan 154.50, daga nan aka samu karin naira biliyan 159.30 da kuma biliyan 180.50 a shekarar 2014 da kuma 2015”

NAN