Home Labarai Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta karyata zargin rashin ciyar da ɗaurararru a Kano

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta karyata zargin rashin ciyar da ɗaurararru a Kano

0
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta karyata zargin rashin ciyar da ɗaurararru a Kano

Hukumar kula da gidajen gyaran hali, reshen jihar Kano ta musanta zargin da ake yi na cewa ba a ciyar da daurarru abinci yadda ya kamata.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya fitar a yau Alhamis, hukumar ta ce babu gaskiya a zargen zargen da ake yadawa kan batun ciyar da daurarrun.

“Hukumar kula da gidajen gyaran hali na shaidawa al’umma cewa, walwala da kula da daurarru shi ne abinda tafi baiwa muhimmanci, kuma wannan hukuma na tabbatar da cewa ana kula dasu duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a yanzu.

“Al’umma na sane da cewa, kwanan nan gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin da ake ciyar da daurarru, an yi hakan ne domin tabbatar da walwalarsu.”

Sanarwar ta ce ba iya kulawa ba kadai, har tabbatarwa ake yi da an koyar da daurarrun sana’o’i tare da ilimantar dasu domin shirya su su koma cikin al’umma.

“Wannan hukuma na kira da al’umma da su yi watsi da irin wadannan rahoto da ake yadawa ga al’umma”. Muna tabbatar da al’umma cewa ana kare hakkin dan adam da daurarru suke da shi”, inji sanarwar.