Home Labarai Hukumar Kwana-kwana ta ceto rayuka 420 da kadarori na N490.6m a Kano

Hukumar Kwana-kwana ta ceto rayuka 420 da kadarori na N490.6m a Kano

0
Hukumar Kwana-kwana ta ceto rayuka 420 da kadarori na N490.6m a Kano

 

Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta ceto rayuka 410, da kadarori wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 490.6, a haɗarin gobara 489 da aka samu a jihar tsakanin Janairu zuwa Afrilu 2022.

Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar, shine ya bada wannan ƙididdiga a wata hira da ya yi da NAN a yau Juma’a a Kano.

Ya ce hukumar kashe gobarar ta amsa kiraye-kirayen ceto 303, yayin da aka gano kiraye-kirayen 94 na ƙarya daga mazauna jihar.

A cewarsa, mutane 59 ne suka rasa rayukansu, inda ya ƙara da cewa dukiyoyin, wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 189.5 sun ƙone a haɗsrurrukan gobarar a tsawon tsakanin wannan lokacin.

“A kwatar shekara ta farko a cibiyoyin kashe gobara 27 da ke jihar, mun ceto mutane 24 da suka fada cikin budadden rijiyoyin, yayin da wasu 13 suka makale a cikin rijiyoyin.

“Har ila yau, hukumar ta kai ɗauki a hadurran tituna 245, yayin da sauran waɗanda aka ceto sun kasance daga gine-ginen da su ka rushe, wutar lantarki, da kuma shadda na banɗakuna, da sauransu,” in ji shi.

Kakakin ya danganta faruwar gobarar da rashin kula da gas ɗin dafa abinci da kuma amfani da na’urorin lantarki marasa inganci.

Yayin da ya bukaci jama’a da su rika kula da wutar girki da kulawa don hana afkuwar gobara, Abdullahi ya gargadi masu ababen hawa da su bi ka’idojin zirga-zirga domin gujewa hadurran mota.

Kakakin ya kuma bukaci iyaye da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da sanya ido a kan ƴaƴan su, musamman a lokacin da suke yin wanka a rafi ko cikin tafki ko wasa a wurare masu hadari.