
Hukumar horas da masu hidimar kasa ta NYSC ta bayyana cewar rukunin B tafiya ta biyu 2017 ya samu koma baya a jihar Binuwai,inda aka mayar da shirin horas da su din daga 16 ga watan Janairun nan zuwa 15 ga watan Fabrairu, an dakatar da shi na wucin gadi.
Hukumar ta bayar da wannan sanarwa ne a shafinta na Facebook a Abuja ranar lahadi Ta bayyana cewar, nan ba da jimawa ba za’a sanya sabuwar ranar da zaa yiwa masu hidimar kasar horo a jihar.
“Hukumar NYSC tana sanar da dukkan masu hidimar kasa, wadan da aka tura jihar Binuwai da Taraba a rukuni na B kuma tafiya ta II, shirin horas da su an dakatar da shi na wani dan lokaci”
“Nan ba da jimawa ba za’a sanya sabuwar ranar da za’a gabatar da shirin horas da su din. A sabida haka hukumar ke bayar da hakurin samun wannan sauyi da aka yi”
A baya dai hukumar ta fitar da ranar 15 Janairu a matsayin ranar da masu karbar horon zasu shiga sansanonin horas da su a dukkan fadin Najeriya.
Jihohinda suke da sansanonin horas da ‘yan hidimar kasar su ne, Abia, Bauchi, Benue, Delta, Enugu, Sokoto, Jigawa, Kaduna, Katsina, Plateau, Lagos, Osun, Oyo, Rivers da kuma FCT.
NAN