Home Labarai Hukumar Sufurin Jiragen ƙasa ta sake ɗage ranar dawo da jigilar layin dogo na Abuja-Kaduna

Hukumar Sufurin Jiragen ƙasa ta sake ɗage ranar dawo da jigilar layin dogo na Abuja-Kaduna

0
Hukumar Sufurin Jiragen ƙasa ta sake ɗage ranar dawo da jigilar layin dogo na Abuja-Kaduna

 

Hukumar kula da harkokin Sufurin Jiragen ƙasa ta Ƙasa, NRC, ta dakatar da shirinta na dawo da jigilar fasinjojin Abuja zuwa Kaduna.

Hukamar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a, mai ɗauke da sa hannun mai Magana da yawunta Mahmood Yakub.

A tuna cewa a cikin wata Maris ne ƴan ta’adda su ka kai hari kan jirgin ƙasan, inda su ka kashe da dama su ka kuma yi awon-gaba da wasu.

Tun daga nan sai NRC ta dakatar da jigilar fasinjojin a tashoshin jirgin ƙasa na daga Abuja zuwa Kaduna.

A baya-bayan nan ne dai hukumar ta yi yunƙurin dawo da jigilar jirgin, amma daga bisani sai ta fasa.

A wannan karon ma, bayan da Hukumar ta sanar da cewa za ta dawo da jigilar jirgin ƙasan a ranar Litinin 23 ga watan Mayu, sai kuma a juya ta sake sanar da cewa ta janye.

Sanarwar ta ce za a sanar da sabuwar ranar dawo da jigilar nan ba da jimawa ba.