Home Labarai Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi barazanar kama Dambazau

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi barazanar kama Dambazau

0
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi barazanar kama Dambazau

 

A jiya Alhamis ne Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC ta yi barazanar kama Manajan-Darakta na Hukumar Kare Hakkin mai Saye, KCPC.

Shugaban PCACC, Mahmoud Balarabe ne ya yi wannan barazanar a Kano, in da ya ce Dambazau, wanda Janar ɗin soja ne mai ritaya, ya ƙi amsa gayyatar da aka yi masa bisa karɓar cin hanci da rashawa.

Balarabe ya ce PCACC ta samu korafe-korafe da dama na zargin cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka da ake yi wa shugaban na KCPC.

“Doka ta umarce mu da mu gayyaci kowane mutum idan aka shigar da kara a kansa.

“Wannan shi ne don tabbatar da cewa an bai wa mutumin damar amsa koken don yin adalci da kuma sauraron shari’a,” in ji shi.

Balarabe ya lura cewa dokar da ta kafa PCACC ta ba ta ikon kama duk wanda ya ƙi amsa gayyatar ta.

“Jami’an tsaron da ke ƙarƙashin mu sun ziyarci ofishinsa domin kama shi, amma aka ce ba ya nan.

“Sun duba ko’ina kuma ba su gan shi ba. Ya kamata ko dai ya girmama gayyatar da muka yi masa ko kuma a kama shi a duk inda muka same shi.

“Gayyatar amsa zarge-zargen ba ya nufin wani yana da laifi. Mun zo nan ne domin mu magance matsalar cin hanci da rashawa da ke addabar al’ummarmu,” Balarabe ya jaddada.