
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta musanta zargin kirkiro karin akwatunan zabe 30,000 ababban zabe na 2019 dake tafe.
Kakakin jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, a ranar Juma’a ya zargi hukumar zabe ta kasa INEC da yunkurin taimakawa magudi a zaben 2019 mai zuwa ta hanyar kirkiro da karn akwatunan zabe 30,000 a wasu yankuna a fadin Najeriya.
Sai dai kuma, a wata sanarwa da hukumar zaben ta kasa INEC ta fitar, ta hannun mai magana da yawun hukumar, Rotimi Oyekanmi, a ranar Lahadi a babban birnin tarayya Abuja, yayi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan batu domin babu gaskiya a cikinsa.
Maimagana da yawun hukumar ya cigaba da cewar, hukumar zaben ta samu sakwannin bukata daga mutane 3,789 na neman karin akwatunan zabe a fadin tarayyar Najeriya.
Acewar hukumar ta baiwa kwamishinoninta na jihohiumarnin da su duba mata su ganin sababbin unguwannin da suka cancanci samun akwatunan zabe, su kuma dubu yuwuwar hakan tare da aiko mata bayani.
Yace ba haka nan hukumar ke kirkiro karin akwatunan zabe ba, har sai ta yi tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki akan harkokin zabe a Najeriya, sannan ta yanke hukuncin kirkiro karin sabbin akwatunan zabe.